- Farashin Dalar Amurka ya ƙaru a kasuwar hada-hadar musayar kuɗi ta gwamnati a ranar Talata, 4 ga watan Yuni, 2024
- Rahoton shafin cinikayyar kudi FMDQ ya nuna Naira ta faɗi zuwa N1,476.95 kan kowace dala idan aka kwatanta da farashin ranar Litinin
- Wannan dai na zuwa ne a lokacin da CBN ke ci gaba da ɗaukar matakai da nufin dawo da ƙimar Naira kan Dalar Amurka a ƙasar nan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kimar kudin Najeriya wanda muka fi sani da Naira ta ragu a kasuwar hada-hadar kuɗi ta gwamnati ranar Talata, 4 ga watan Yuni, 2024.
Dalar Amurka ta ƙara tsada, inda ta koma N1,476.95 kan kowace Dala guda a kasuwar gwamnati jiya.

Kara karanta wannan
Tsohon gwamnan CBN ya shiga tasku, kotu ta ƙwace manyan kadarorinsa na N11.1bn

Naira ta karye a kan Dalar Amurka
Bayanai daga shafin kula da hada-hadar musayar kuɗin waje FMDQ na ranar Talata ya nuna cewa ƙimar Naira ta ragu da Kobo 83.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Tribune Nigeria ta tattaro cewa hakan na nufin Naira ta faɗi da kaso 0.06% idan aka kwatanta da farashin N1,476.12/1$ da aka yi musanya ranar Litinin.
Ciniki ya karu a kasuwar gwmanati
Har ila yau, adadin kuɗin da aka yi cinikayyarsu ranar Talata ya ƙaru zuwa Dala miliyan 236.99 daga Dala miliyan 121.87 da aka yi hada-hada da su ranar Litinin.
Bugu da ƙari, a kasuwar masu zuba jari (I&E), an yi hada-hadar musanya kuɗin Najeriya a farashi tsakanin N1,500.00 da N1,362.15 kan kowace Dala.
Legit Hausa ta fahimci cewa a halin yanzun ƙimar Naira na faɗuwa wani lokacin kuma ta farfaɗo a kasuwar gwamnati da kasuwar bayan fage ta ƴan canji.

Kara karanta wannan
Rahoto: Yajin aikin 'yan ƙwadago ya jawo Najeriya ta yi asarar Naira biliyan 149
Bankin CBN ya ɗauki matakan karya Dala
Wannan na zuwa ne duk da matakan da babban bankin Najeriya (CBN) yake ci gaba da ɗauka da nufin farfaɗo da darajar Naira.
Farashin Naira dai na da tasiri a rayuwar ƴan Najeriya ta yau da kullum idan aka yi la'akari da yadda ake fama da tsadar kayayyakin abinci da sauransu, rahoton Guardian.
CBN ya umarci sabunta lasisin ƴan canji
A wani rahoton kuma kun ji cewa babban bankin ƙasa CBN ya yi wasu sababbin sauye-sauye domin inganta ayyukan ƴan canji.
CBN ya umarci halastattun ƴan canaji su sabunta lasisin aiki kuma ya cire masu dokar ajiye wasu adadin kudi kafin a ba su lasisi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllboJ5hJZmm5qqkZ%2Bus3nNmqCrmV2prm6ywJ2gZpyRoa6zecCmrKujkWLBonnKmqmaZaSorqWtjJpkp5mamr%2BqxcBo