• Hotunan iyalan AGF Abubakar Malami tare da sabuwar amaryarsa, Nana Hadiza Muhammadu Buhari sun matukar kayatarwa
  • A hotunan da Surayya KofarMata ta wallafa a shafinta na Instagram, an ga Nana Hadiza cikin iyalansa inda uwargida ta bayyana cike da annashuwa
  • A data daga cikin hotunan, Uwargida Aisha Malami ce tsaye tare da amarya Hadiza Buhari Malami cikin farin ciki

Sabbin hotunan Nana Hadiza Muhammadu Buhari a cikin iyalan ministan shari'ar Najeriya kuma antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, SAN, sun matukar kayatar da jama'a.

A kyawawan hotunan da @surrykmata ta wallafa a shafinta na Instagram, an ga sabuwar amaryar tare da mijinta, a wani hoton kuma tare da uwargidanta yayin da wani ya bayyana tana cikin iyalan.

Kara karanta wannan

2023: Ku kwantar da hankali, za fa ku ci zaben nan, Buhari ga Tinubu da Shettima

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

AGF Malami yayi wuff da diyar shugaba Buhari, hotuna suna bayyana

A wani labari na daban, a yau ranar 8 ga watan Yulin 2022 ne aka daura auren Nana Hadiza Muhammadu Buhari da AGF Abubakar Malami, SAN.

An daura auren a Abuja yayin da aka yi karamin biki a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari dake Abuja tare da 'yan uwa da abokan arziki.

Daya daga cikin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya tabbatar da hakan.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlkbX5zgY9morKZp5bEorqMoaatrZ6Wu260wJ2gs5ldl8KprdGiZJyhm567brXYmqOapl2irq2tzKJkrK2eYriixcCtmKtlpayus7PInZhmrJFiuKK%2BwZ6rmmWYlruvwYyboJuama7CcA%3D%3D