Wani hoto dake yawo a shafukan yanar gizo ya nuna wasu gungun mata da Sojojin kasar Uganda suka sanya su yin tsirara bayan sun ci lardin su da yaki.

Jaridar Tuko ta bayyana cewar a daren Asabar 26 ga watan Nuwamba ne rundunar mayakan soja na kasar Uganda wanda aka fi sani da suna UPDF tare da rundunar yansandan kasar suka kai wani hari masarautan Obusinga bwa Rwenzururu bayan an samu wani rahoton cewar Sarkin Obusinga bwa Rwenzururu ya shirya wasu Sojojin Tawariyya da zasu taimaka masa wajen samar da sabuwar kasar Obusinga bwa Rwenzururu daga Uganda.

KU KARANTA: Ko ka taɓa ganin masai na Zinari? (HOTUNA)

Kimanin mutane 55 aka ruwaito sun rasa rayukansu daga dukkanin bagarorin dake fafatawa a yakin bayan an kwashe awanni da dama ana musayar wuta.

Su kuwa gungun matan an kwaso su ne daga fadar mai martaba sarkin Obusinga bwa Rwenzururu, daga sai Sojojin suka garzaya wani wuri dasu inda basu bayyana ba.

Zaku iya samun mu a shafin Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9j29tb3BiYr%2Bqt8icoGaxkWJyc4HCclxrbWlorq24xGaYZl1iarB3cZFucHKZo5a%2FbsHGmqWdmV2pwKK3wKegp2WXrK6uusCtoGackWLGorqMrZiwmaKexrqtjaGrpqQ%3D