- Fitaccen mawaki, kuma mai shirya fina-finan Hausa, Ali Jita, ya yi magana kan halin kuncin rayuwa da jarumi Adam A Zango yake ciki
- Ali Jita ya ce Adamu mutumin kirki ne kuma lokaci ya yi da ya kamata 'yan fim da mawaka duk su fito su ja shi a jika tare da neman mafita
- Idan ba a manta ba, mawaki Zango ya saki wani bidiyo wanda yake nuna irin butulcin da ya ce wasu 'yan Kannywood sun yi masa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Fitaccen mawaki, kuma mai shirya fina-finan Hausa, Ali Jita, ya yi magana kan halin kuncin rayuwa da jarumi Adam A Zango yake ciki.

Kara karanta wannan
"Ban son zama ubangida" Malam El-Rufa'i ya mayar da martani kan abin da ke faruwa a Kaduna

Ali Jita wanda ya yi martani kan bidiyon Zango a shafinsa na TikTok a ranar safiyar ranar Litinin, ya ce lokaci ya yi da ya kamata 'yan Kannywood su taimaki Adam A Zango.
"Daukaka ba alkairi ba ce" Adam A Zango
Mawaki Zango ya dauki wani faifan bidiyo wanda ya fadawa duniya irin jarabawar rayuwar da yake fuskanta, kamar yadda shafin Arewa Focus ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na ba mutane da dama gudunmawa a Kannywood, amma basu taba yabo na ba sai dai su yabi wani daban saboda ni wulakantacce ne a wajensu."Daukaka ba alkairi bace, kullum kana nunawa duniya kana da kudi kuma ba ka da matsala, amma a zahirance kafi kowa fuskantar kalubale, kuma babu hali ka fito ka fada."Wadanda Adam Zango ya taimaka a Kannywood

Kara karanta wannan
Adam A Zango ya fitar da sabon faifan bidiyo kan halin da ya ke ciki, ya yi godiya
Adam Zango ya lissafa wadanda ya ba kyautar mota a masana'antar da suka hada da Falalu A Dorayi, Sadiq N. Mafia, Tahir I. Tahir, Abubakar Sani, Kabiru, Rabiu, Umar Big Show.
Wadanda ya taimaka suka samu daukaka a Kannywood kamar yadda ya zayyana, sun hada da:
"Fati Nijar, Nazifi Asnanic, Zainab Raga, Zainab Indomie, Ali Jita, Isah Feruskan, Umar Big Show, Ado Gwanja, Ussaini Danko, Umar M. Shareef da Sadiq Sani Sadiq.""Adamu mutumin kirki ne" - Ali Jita
A wannan gabar ne, mawaki Ali Jita ya yi martani kan kalaman na Zango, inda ya gasgata dukkanin abin da ya fada tare da cewa:
"Adamu mutumin kirki ne kuma zuciyarshi tana da kyau, ba shakka ya taimake ni da sauran wadanda ya lissafa. Ina amfani da wannan dama in bashi hakuri a madadinmu gaba daya."Ina ganin yanzu lokaci ya yi da ya kamata 'yan fim da mawaka duk mu fito mu ja Adamu a jiki, mu gane matsalolin da aka samu a baya domin a gyara su."
Kara karanta wannan
Ali Nuhu ya fito ya gayawa duniya halin da Adam A. Zango ya samu kansa a ciki
Ali Jita ya yi nuni da cewa dan Adam tara yake bai cika goma ba, don haka za su zauna da Zango a kungiyance domin yi wa dukkanin tufkar hanci.
"Adamu na cikin koshin lafiya" - Ali Nuhu
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa jarumi Ali Nuhu ya fitar da sanarwa a shafinsa na Facebook da ta nuna cewa jarumi Adam A Zango na nan cikin koshin lafiya.
Ali Nuhu ya yi wannan sanarwar ne biyo bayan rubututtuka da bidiyo da mawaki Zango ya wallafa a soshiyal midiya wanda yake nuna irin mawuyacin halin da yake ciki a yanzu.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC3wKelsq%2BfpLFwfZRxbnFwY2LHonnMrmStmZmirqyxjKyfomWRobZutsitmGaxkWK6orPAp6uuZZuWu260wKWgp2WUlnqisMCmZJplqpa7qLuMspiknV2Ytqy1jg%3D%3D